Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya ya gargadi matasa da su guji bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen tayar da rikici ko haifar da tashin hankali.
Da yake jawabi a wani babban taron tattaunawa kan shugabancin matasa da harkokin tsaro a Abuja, Sufeto Janar din ya ce amfani da matasa wajen rikici na iya lalata makomarsu, yayin da wadanda suka jefa su cikin rikicin za su iya sasanta daga baya.
Ya shawarci matasa da su mayar da hankali wajen neman ilimi, sana’o’i, kimiyya, kirkire-kirkire da ayyukan ci gaban al’umma, maimakon shiga ta’addanci ko rikicin siyasa.
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ce ta shirya taron a matsayin wani bangare na bikin ranar matasa ta duniya ta wannan shekara.
Sufeto Janar din ya kuma bukaci matasa da kada su bari a yaudare su da bambancin kabila, addini, yanki, al’ada ko siyasa, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da wadannan bambance-bambance wajen lalata makomar matasa ba.