Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ta tura kudaden da ta kwato zuwa Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND), domin tallafawa ilimin daliban kasar.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai karin bayani bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da Shugaba Tinubu ya jagoranta a Abuja.
A cewar ministan, umarnin ya hada da kudaden da EFCC ta kwato, ribar hannun jari da ba a karba ba, da kuma wasu kudaden asusun da ba a taba amfani da su ba.
Ya ce manufar matakin ita ce kara wa NELFUND karfin kudi domin hukumar ta samu damar biyan bukatun daliban da ke karuwa a fadin Najeriya.
Alausa ya bayyana cewa FEC ta amince da umarnin shugaban kasar, inda ya ce gwamnati na son tabbatar da cewa kudaden da ake samu daga wasu kadarori da kudaden da aka kwato sun taimaka wajen bunkasa ilimi.
Sai dai ministan ya bayyana cewa ba za a tura kudaden da ke gaban kotu ko wadanda ake takaddama a kansu ba har sai an kammala shari’o’in da suka shafe su.
Ya kuma ce ana duba wasu dokoki domin tabbatar da cewa tsarin tura kudaden zuwa NELFUND ya kasance bisa ka’ida da tanadin doka.
NELFUND dai hukuma ce da gwamnatin tarayya ta kafa domin samar da tallafin lamuni ga daliban manyan makarantu a Najeriya, musamman wajen taimaka musu wajen biyan kudaden karatu da sauran bukatun ilimi.