Ƴar Najeriya, Maryam Ibrahim Dan Azumi yar asalin Jihar Gombe ta samu matsayi na farko a gasar musabaƙar Alƙur’ani mai girma ta Hizb 60 tare da Tafsiri, bayan da ta yi fice wajen karatun Alƙur’ani da fahimtar ma’anoni da tafsirinsa.
A ɓangaren maza kuwa, Muhammad Abdullahi Marafa, ɗan Jihar Zamfara, ya samu matsayi na biyar a gasar.
Wannan nasara ta ƙara ɗaukaka sunan Najeriya a fagen gasar Alƙur’ani ta duniya, tare da nuna irin hazaka da ƙoƙarin matasan ƙasar wajen haddace Littafin Allah da kuma fahimtar saƙonnin da yake ƙunshe da su.
Gasar ta bana ta samu halartar masu fafatawa daga ƙasashe 133 na duniya, lamarin da ya ƙara muhimmancin nasarar da ƴan Najeriya suka samu.
Nasarar Maryam Ibrahim Dan Azumi da matsayi na biyar da Muhammad Abdullahi Marafa ya samu sun zama abin alfahari ga Najeriya, musamman a fannin haddar Alƙur’ani da ilimin tafsiri.