Rundunar Sojin Najeriya ta sauya tsarin tsaro a Ƙaramar Hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto da yankunan da ke makwabtaka da ita, bayan samun bayanan sirri cewa ’yan ta’addan da suka kai hari a yankin a makon da ya gabata har yanzu suna kusa.
Babban Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Bemgha Koughna, ya kai ziyarar duba halin tsaro a Kebbe tare da ganawa da shugabannin al’umma da mazauna yankin.
Rundunar ta ce an sake tsara dabarun tsaron yankin domin hana ’yan ta’adda sake kutsawa cikin al’ummomi da kuma ƙara kare wuraren da ke cikin haɗari a hanyar Sokoto zuwa Kebbi.
Jami’an sojin sun kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa suna cikin shirin ko-ta-kwana domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da buƙatar al’umma su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai.