Ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sun taya Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar sake lashe zaɓen gwamna.
Hukumar INEC ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu ƙuri’u 511,067.
Obi ya bayyana cewa sakamakon zaɓen ya nuna cewa ikon zaɓar shugabanni yana hannun jama’a. Ya kuma yaba wa matasan Osun kan yadda suka kare ƙuri’unsu cikin lumana.
Shi kuwa Saraki ya bayyana nasarar Adeleke a matsayin wata ƙuri’ar amincewa da al’ummar jihar suka sake ba shi bayan shekaru huɗu na mulki.
Saraki ya buƙaci Adeleke da ya yi amfani da wa’adinsa na biyu wajen ƙara inganta ayyukan gwamnatinsa tare da tabbatar da amincewar da al’ummar Osun suka sake ba shi.