Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa ba zai taɓa goyon bayan jam’iyyar APC ba.
Davido ya bayyana hakan ne a wasu saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Osun na 2026.
Mawakin, wanda ɗan uwan Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ne, ya kuma yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tsawatar wa wasu daga cikin magoya bayansa.