Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn kori mijina bayan shekaru 19 yana aiki, har yanzu yana tsare...

An kori mijina bayan shekaru 19 yana aiki, har yanzu yana tsare – Matar tsohon jami’in DSS

Hauwa Mundi, matar tsohon ma’aikacin Hukumar DSS, Ibrahim Bichi, ta ce an kori mijinta daga aiki bayan ya shafe shekaru 19 yana yi wa hukumar aiki, amma har yanzu yana tsare ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Hauwa Mundi, matar tsohon ma’aikacin Hukumar DSS, Ibrahim Bichi, ta ce an kori mijinta daga aiki bayan ya shafe shekaru 19 yana yi wa hukumar aiki, amma har yanzu yana tsare ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Mundi, wadda ’yar jarida ce, ta ce an tsare Bichi tun ranar 3 ga Yunin 2026 bayan an umarce shi da ya je hedikwatar DSS a Abuja domin halartar wani horon yaƙi da ta’addanci na kwanaki biyu.

Ta ce daga baya ta gano cewa an shigar da ƙara a kansa ne saboda wasu kalaman da ya wallafa a kafafen sada zumunta, musamman kan batun Hausawa da Fulani da kuma tarihin Shehu Usman Ɗan Fodio.

A cewarta, Bichi ya yi magana kan yadda ake amfani da kalmar “Hausa-Fulani” wajen siyasa, tare da bayyana ra’ayinsa kan wasu abubuwan da suka faru a lokacin jihadin Ɗan Fodio.

Mundi ta ce tun bayan tsare shi, tana ziyartarsa duk mako, amma babu wani bayani da aka ba su kan lokacin da za a sake shi ko kuma a gurfanar da shi a kotu.

Ta ce daga baya sun nemi taimakon lauya, amma DSS ta ƙi bai wa lauyan damar ganawa da Bichi, duk da wasiƙun da aka aika wa hukumar da kuma Ministan Shari’a.

Matar ta ce a ranar 28 ga Yulin 2026 ne aka sanar da Bichi cewa an kore shi daga aikin DSS, bayan ya shafe shekaru 19 yana aiki ba tare da an taɓa ba shi wata sanarwar gargadi ba.

Ta bayyana cewa babban abin da take nema shi ne a bayyana dalilin tsare mijinta a fili, ko kuma a sake shi idan babu wani laifi da ya kamata a gurfanar da shi a kai.

Mundi ta kuma ce tsare mijinta ya jefa iyalinsu cikin mawuyacin hali, musamman ganin cewa tana kula da ’ya’yansu ita kaɗai, yayin da suke fuskantar matsalar kuɗin makaranta da sauran bukatun gida.

Ta ce Bichi ya taɓa fama da matsalar damuwa bayan abin da ya gani a lokacin da yake aiki a Maiduguri wajen yaƙi da Boko Haram, tana mai cewa DSS da gwamnatin tarayya ya kamata su yi adalci tare da bayyana gaskiyar lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments