Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai’Yan sanda sun kama ɗan majalisa da wasu mutum 146 da ake zargin ’yan daba ne a Osun

’Yan sanda sun kama ɗan majalisa da wasu mutum 146 da ake zargin ’yan daba ne a Osun

Rundunar ’yan sandan Jihar Osun ta kama wani ɗan majalisar dokokin jihar, Abiola Inaolaji, tare da wasu mutane 146 da ake zargin ’yan daba ne a Ikire, Ƙaramar Hukumar Irewole.

Rundunar ’yan sandan Jihar Osun ta kama wani ɗan majalisar dokokin jihar, Abiola Inaolaji, tare da wasu mutane 146 da ake zargin ’yan daba ne a Ikire, Ƙaramar Hukumar Irewole.

Kakakin rundunar, DSP Abiosun Ojelabi, ya tabbatar da kamen a Osogbo ranar Asabar, yana cewa an kama ɗan majalisar ne a wani samame da jami’an tsaro suka gudanar.

Inaolaji, wanda ke wakiltar mazabar Irewole/Isokan kuma mamba ne na jam’iyyar Accord, an kama shi ne yayin da ake ƙara tsaurara matakan tsaro gabanin zaɓen gwamnan jihar.

Rundunar ta ce matakin na daga cikin ayyukan da ake yi domin hana duk wani abu da ka iya kawo cikas ga sahihanci da zaman lafiyar zaɓen.

A wani bidiyo da ya yaɗu, wani mutum mai suna Ibrahim ya bayyana cewa shi ne ya taimaka wajen kawo mutane 146 daga wasu jihohin makwabta zuwa Osun domin su kada ƙuri’a a zaɓen.

’Yan sanda ba su bayyana ƙarin bayani kan mutanen da aka kama ko irin matakin da za a ɗauka a kansu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments