Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSarkin Musulmi ya ayyana yau Juma’a a matsayin 1 ga Rabi’ul Auwal...

Sarkin Musulmi ya ayyana yau Juma’a a matsayin 1 ga Rabi’ul Auwal 1448H

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana Juma’a, 14 ga Agusta 2026, a matsayin ranar farko ta watan Rabi’ul Auwal 1448H a Najeriya.

Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis, 13 ga Agusta.

A cewar sanarwar, Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini da Kwamitin Duban Wata na Majalisar Sarkin Musulmi sun samu rahotannin ganin jinjirin watan Rabi’ul Auwal daga sassa daban-daban na Najeriya.

Rahotannin ganin watan sun zo ne a ranar Alhamis, wadda ta yi daidai da 29 ga Safar 1448H.

Bayan tabbatar da rahotannin, Sarkin Musulmi ya amince da su tare da ayyana Juma’a 14 ga Agusta a matsayin 1 ga Rabi’ul Auwal 1448H.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments