Malamin addinin Musulunci daga Kaduna, Dr. Ahmad Gumi, ya bayyana goyon bayansa ga amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen tallafa wa matasa da sauran masu buƙatar aure.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gumi ya ce irin wannan tallafi ya halatta, musamman a jihohin da ke gudanar da harkokinsu bisa tsarin Shari’a.
Ya bayyana cewa idan gwamnati na ƙoƙarin rage matsalolin karuwanci, zina da sauran abubuwan da addini ya haramta, tallafa wa waɗanda ke son yin aure na iya kasancewa wani ɓangare na shugabanci nagari.
Malamin ya ƙara da cewa tallafa wa matasan da ke cikin tsananin buƙatar aure, da kuma mata waɗanda ke da ƙarancin mazajen da suka cancanci aure, na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen rage wasu matsalolin zamantakewa.