Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiIyalan mutum 7 sun tsallake rijiya da baya a jihar Niger

Iyalan mutum 7 sun tsallake rijiya da baya a jihar Niger

A Jihar Niger, wani iyali mai mutum bakwai sun tsira daga mutuwa bayan ambaliyar ruwa ta mamaye gidansu a Mohammed Inuwa Wushishi Housing Estate da ke Minna.

A Jihar Niger, wani iyali mai mutum bakwai sun tsira daga mutuwa bayan ambaliyar ruwa ta mamaye gidansu a Mohammed Inuwa Wushishi Housing Estate da ke Minna.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2 na dare bayan ruwan sama mai ƙarfi, inda wani ɓangare na ɗakin da iyalan ke kwana ya rufta.

Blessing Afiku, wadda ke zaune a yankin, ta ce ambaliyar ta tafi da awaki 12 daga cikin 15 da take kiwo, tare da lalata injin ɗinki, kayan sawa da kayan abinci.

Wasu mazauna yankin sun ce ruwan ya kai tsayin ƙirji a cikin gidajensu, lamarin da ya tilasta wasu iyalai guduwa zuwa masallatai domin neman mafaka.

Mazaunan sun danganta ambaliyar da toshewar hanyoyin ruwa, ciki har da ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, tare da yin kira ga gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki.

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Niger (NSEMA) ta shawarci mazauna kusa da magudanan ruwa, rafuka da bakin koguna da su koma wuraren da suka fi tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments