Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAmbaliyar ruwan sama ta lalata gidaje a jihar Nasarawa

Ambaliyar ruwan sama ta lalata gidaje a jihar Nasarawa

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da kadarori a wasu sassan Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi da safiyar Alhamis.

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da kadarori a wasu sassan Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi da safiyar Alhamis.

Unguwar Nungu, Millionaires Quarters da Bukan Sidi na daga cikin wuraren da lamarin ya fi shafa, inda ruwan da ya taso daga magudanan ruwa da suka toshe ya shiga gidajen jama’a.

Wani mazaunin Unguwar Nungu, Cheke Emmanuel, ya ce ambaliyar ta rusa wasu katangu da wani gini, tare da lalata kayayyakin mazauna yankin.

Ya ce babu wanda ya rasa ransa, amma ambaliyar ta jefa jama’a cikin firgici tare da tilasta wasu ficewa daga gidajensu.

Emmanuel ya danganta lamarin da rashin ingantattun magudanan ruwa da kuma lalacewar titunan Ember A da Ember B, inda ya yi kira ga gwamnati ta gaggauta gyara hanyoyin da magudanan.

A nata bangaren, Kwamishiniyar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta jihar Nasarawa, Princess Margaret Elayo, ta gargadi mazauna yankunan da ambaliya ke barazana gare su da su koma wuraren da suka fi tsaro.

Elayo ta ce toshewar hanyoyin ruwa da shara, rashin ingantattun magudanan ruwa da kuma cike tafkuna da wuraren buɗe ido sun taimaka wajen haddasa ambaliyar.

Ta kuma bayyana cewa Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanya Lafia, Da ma da wasu sassan jihar cikin wuraren da ke fuskantar barazanar ambaliya mai tsanani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments