Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSokoto ta ware Naira biliyan 1.7 domin sayen babura 1,000 don yaƙi...

Sokoto ta ware Naira biliyan 1.7 domin sayen babura 1,000 don yaƙi da ’yan bindiga

Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kashe Naira biliyan 1.759 domin sayen babura 1,000 kirar Bajaj da za a bai wa hukumomin tsaro domin ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga a jihar.

Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kashe Naira biliyan 1.759 domin sayen babura 1,000 kirar Bajaj da za a bai wa hukumomin tsaro domin ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga a jihar.

An amince da kuɗin ne a taron majalisar zartarwar jihar karo na shida, wanda Mataimakin Gwamna, Idris Muhammad Gobir, ya jagoranta.

Baburan za su ƙara wa jami’an tsaro ƙarfin gudanar da ayyuka a yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.

Baburan za su kasance ƙarin kayan aiki ga motocin sulke 62 da gwamnatin jihar ta saya kan Naira biliyan 27, waɗanda aka raba wa hukumomin tsaro domin gudanar da ayyukan tsaro.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Gwamnan Sokoto, Abubakar Bawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Sokoto.

A bangaren ilimi, majalisar ta amince da Naira miliyan 723.17 domin gyaran Government Technical College da ke Runjin Sambo, yayin da aka ware Naira miliyan 498.99 domin gyaran A.A. Raji Special School.

Haka kuma, an amince da Naira miliyan 489.32 domin gyaran kashi na farko na College of Nursing Sciences, yayin da Naira miliyan 229.36 aka ware domin gyaran dakunan kwanan ɗalibai na College of Basic and Remedial Studies.

A fannin noma, majalisar ta amince da Naira miliyan 174.64 domin gyaran gidajen ma’aikata da inganta katangar College of Agriculture and Animal Science da ke Wurno.

Haka kuma, an ware Naira miliyan 133.67 domin gina katanga a Wamakko Primary Health Centre.

Gwamnatin ta kuma amince da Naira miliyan 93.88 domin samar da kayan koyar da sana’o’i a cibiyoyin koyar da sana’a na mata 46 da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 23.

A fannin ruwa kuma, majalisar ta amince da Naira miliyan 90.208 domin sayen bututun PVC da kayan aikin famfo don kula da tsarin samar da ruwan sha guda 142 a ƙananan hukumomin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments