Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiRundunar ’Yan Sandan Kano ta kama mutane uku bisa zargin satar adaidaita...

Rundunar ’Yan Sandan Kano ta kama mutane uku bisa zargin satar adaidaita sahu da mota

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu wajen satar adaidaita sahu da motoci a wasu sassan jihar da maƙwabtan jihohi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 11 ga Agusta, 2026.

Rundunar ta ce ta kama Muhammad Sani, mai shekaru 23, bisa zargin satar adaidaita sahun wani direba a titin Hadejia.

Binciken da aka gudanar ya kai jami’an rundunar har zuwa Jihar Katsina, inda aka cafke Aminu Sa’ad, mai shekaru 33, tare da kwato adaidaita sahu guda huɗu.

A wani samame kuma, jami’an rundunar sun kama Isah Yusuf, mai shekaru 23, a Rijiyar Lemo, inda aka samu wata mota kirar Pontiac da ake zargin an sace daga Jihar Taraba.

A cewar rundunar, an kai motar zuwa Jamhuriyar Nijar kafin daga bisani aka dawo da ita Najeriya.

Rundunar ta ce an mayar da adaidaita sahu huɗun ga masu su, yayin da ake ci gaba da bincike kan waɗanda aka kama da kuma ƙoƙarin gano mai motar Pontiac domin ya gabatar da shaidar mallakarta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments