Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 21 ga Satumba, 2026 domin ci gaba da sauraron ƙarar da ke kalubalantar cancantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Ƙungiyar Centre for Reform and Public Advocacy ce ta shigar da ƙarar, inda take ƙalubalantar cancantar Tinubu bisa zargin cewa an gabatar da takardun shaidar karatu da kuma takardar NYSC da ake ikirarin ba sahihai ba ne ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a zaɓen 2023.
Shugaba Tinubu, INEC da Chicago State University na daga cikin waɗanda aka haɗa a matsayin waɗanda ake ƙara a shari’ar mai lamba FHC/K/CS/312/2026.
Ana sa ran zaman kotun na ranar 21 ga Satumba zai ci gaba da duba batutuwan da ƙarar ta gabatar da kuma matakan da suka dace a shari’ar.