Dakarun Bataliya ta 17 na Rundunar Sojin Najeriya sun dakile wani shirin kai hari da wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne suka shirya a Karamar Hukumar Charanchi ta Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne bayan da rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:20 na safe ranar 9 ga Agusta, inda aka sanar da ita cewa wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne sun taru a kusa da ƙauyen Kaddanya da ke yankin.
A cewar rahoton Zagazola Makama a shafin X, dakarun da ke sansanin Radda sun gaggauta mayar da martani kan kiran tare da tura jami’ansu zuwa wurin.
Sojojin sun gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar jami’an Rundunar Ƴansandan Najeriya daga Kankia da Charanchi, da kuma jami’an Katsina State Community Watch Corps (KSCWC).
Haɗin gwiwar jami’an tsaron ya taimaka wajen dakile shirin harin tare da hana waɗanda ake zargin ƴan ta’addan cimma burinsu.
Bayan nasarar aikin, dakarun sojin sun ƙara mamaye yankin ta hanyar gudanar da sintiri mai ƙarfi a wurare daban-daban.
Rundunar ta ce manufar sintirin ita ce hana waɗanda ake zargin ƴan ta’addan samun damar gudanar da wani hari ko wani nau’in ta’addanci a yankin.