Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHukumar CAF ta tabbatar da jadawalin manyan gasannin Afirka na 2026/27

Hukumar CAF ta tabbatar da jadawalin manyan gasannin Afirka na 2026/27

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, CAF, ta tabbatar da ranakun gudanar da manyan gasannin nahiyar na kakar 2026/27, tare da bayyana ƙasashen da za su karɓi bakuncinsu.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, CAF, ta tabbatar da ranakun gudanar da manyan gasannin nahiyar na kakar 2026/27, tare da bayyana ƙasashen da za su karɓi bakuncinsu.

Gasar cin kofin Afirka ta 2027, wadda Kenya, Tanzania da Uganda za su karɓi bakunci, za a gudanar da ita daga 19 ga Yuni zuwa 17 ga Yuli, 2027, yayin da wasannin neman gurbin shiga gasar za su fara a watan Satumba na 2026.

A ranar 8 ga Nuwamba, 2026, birnin Tshwane na Afirka ta Kudu zai karɓi bakuncin CAF Super Cup, inda zakaran Champions League, Mamelodi Sundowns, zai kara da zakaran Confederation Cup, USM Alger.

A bangaren matasa, Ghana za ta karɓi bakuncin gasar U-20 ta Afirka a watan Fabrairu da Maris 2027, yayin da Morocco za ta karɓi bakuncin gasar U-17 a watan Afrilu da Mayu. Masar kuma za ta karɓi bakuncin gasar U-23, wadda za ta kasance hanyar neman gurbin shiga gasar Olympics ta Los Angeles 2028.

CAF ta kuma bayyana cewa Morocco za ta karɓi bakuncin gasar Futsal ta Afirka daga 12 zuwa 21 ga Oktoba 2026, yayin da Senegal za ta karɓi bakuncin gasar Beach Soccer a watan Nuwamba.

A gasannin kungiyoyi kuwa, zagayen farko na neman gurbin shiga CAF Champions League da Confederation Cup na 2026/27 zai gudana daga 4 zuwa 6 ga Satumba, yayin da wasannin dawowa za su gudana daga 11 zuwa 13 ga Satumba 2026.

CAF ta ce tabbatar da jadawalin da wuraren gudanar da gasannin zai taimaka wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, ‘yan wasa, masu tallafawa da masu kallo wajen shirya yadda ya kamata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments