Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama mutum biyar da ake zargi da gudanar da rabo da kuma sayar da maganin gargajiya ba tare da izini ba a yankin Challawa.
Rundunar ta gargadi jama’a da kungiyoyi da su daina gudanar da ayyukan rabon magunguna ba tare da sahalewar hukumomin da abin ya shafa ba.
Rundunar ta ce matakin ya biyo bayan korafe-korafe da koke-koken al’umma kan lamarin, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Laraba, ya ce jami’an rundunar 52 Police Mobile Force (PMF) da ke Challawa sun tare wasu mutum shida da ke da alaka da Brother Paul Legacy Foundation a harabar Cocin ECWA da ke bayan sansanin 52 PMF a Challawa a ranar 4 ga Agustan 2026.
Kiyawa ya ce mutanen, karkashin jagorancin Simon Gbaaondo mai shekaru 50 daga Karu a Jihar Nasarawa, suna ba mutane maganin gargajiya da ba a tantance ingancinsa ba.
Ana bayar da maganin kyauta, sannan ana sayar da shi ga dimbin mazauna yankin Panshekara da suka taru a cocin, ba tare da amincewar hukumomin da ke kula da harkokin lafiya ba.
Ya kara da cewa an gayyaci mutumin da ya karbi bakuncin mutanen a harabar cocin domin taimakawa bincike kan yadda aka gudanar da wannan aiki ba tare da izini ba.
Kakakin rundunar ya ce an fara kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Panshekara kafin daga bisani a mika shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na rundunar jihar, inda ake ci gaba da binciken mutum biyar daga cikin wadanda ake zargin.
Sanarwar ta ce: “Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano karkashin jagorancin CP Ibrahim Adamu Bakori ta gargadi daidaikun mutane da kungiyoyi da su guji rarraba magunguna, magungunan gargajiya ko gudanar da ayyukan jinya ba tare da cikakken izini da tantancewa daga Gwamnatin Jihar Kano, NAFDAC da sauran hukumomin lafiya masu ruwa da tsaki ba.”
Rundunar ta ce irin wadannan ayyuka na jefa lafiyar jama’a da tsaro cikin hadari, musamman idan aka tara mutane da yawa a wuri guda.
Kiyawa ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da zaman lafiya, yana mai cewa ba za ta lamunci duk wani aiki da zai iya jefa lafiyar jama’a ko zaman lafiya cikin hadari ba.