Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaPDP ta samu koma baya a Gombe yayin jiga-jiganta biyu suka yi...

PDP ta samu koma baya a Gombe yayin jiga-jiganta biyu suka yi murabus

Jam’iyyar PDP ta sake fuskantar koma baya a Jihar Gombe bayan wasu manyan jiga-jiganta guda biyu sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

Waɗanda suka yi murabus sun haɗa da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Funakaye, Alhaji Ibrahim Yusuf, da kuma mataimakin sakataren PDP na Jihar Gombe, Mohammed Babani Bajoga.

A cikin wasikar murabus ɗinsa mai ɗauke da kwanan watan 2 ga Agusta, 2026, Ibrahim Yusuf ya sanar da cewa ya daina kasancewa mamba a PDP nan take, yana mai cewa ya yanke wannan hukunci ne bayan dogon nazari da kuma wasu dalilai na kashin kansa.

Hakazalika, Mohammed Babani Bajoga ya sanar da murabus ɗinsa a wata wasika mai kwanan watan 3 ga Agusta, 2026, inda ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar bisa raɗin kansa bayan yin nazari kan wasu batutuwa da suka shafe shi.

Duk da haka, babu ɗaya daga cikin tsofaffin jami’an jam’iyyar da ya bayyana takamaiman dalilin ficewarsa ko kuma jam’iyyar siyasar da zai koma.

Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa a Jihar Gombe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments