Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeYariman Saudiyya ya bukaci Trump ya guji ƙara rura rikici da Iran

Yariman Saudiyya ya bukaci Trump ya guji ƙara rura rikici da Iran

Wani rahoto da Axios ya fitar ya ce Yariman Saudiyya kuma Firayim Minista, Mohammed bin Salman, ya roƙi Shugaban Amurka, Donald Trump, da ya guji ɗaukar matakan da za su ƙara tsananta rikicin da ke tsakaninsa da Iran.

Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin Saudiyya ta nuna damuwa kan yiwuwar faɗaɗa rikicin, musamman bayan samun bayanan cewa Amurka na nazarin yiwuwar kai hare-hare kan wasu cibiyoyin makamashi na Iran.

A cewar rahoton, Riyadh ta nemi ƙarin bayani kan irin waɗannan matakai da kuma tasirin da za su iya yi ga tsaron yankin Gabas ta Tsakiya da kasuwar makamashi ta duniya.

A gefe guda kuma, gwamnatin Iran ta yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani mai tsauri idan Amurka ko Isra’ila suka kai mata wani hari, lamarin da ke ƙara nuna fargabar yiwuwar faɗaɗar rikicin a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments