Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya buƙaci al’ummar jihar da ka da su siyasantar da matsalar tsaro, maimakon haka su ƙara yin addu’ar samun zaman lafiya tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin dawo da zaman lafiya.
Radda ya bayyana hakan ne a yayin bikin Yaumul Shukur na 2026, wanda ake gudanarwa domin tunawa da haɗewar tsoffin lardunan Katsina da Daura a shekarar 1934. Ya ce matsalar tsaro ta shafi kowa, don haka tana buƙatar haɗin kai da addu’a, ba anfani da ita wajen siyasa ba.
Gwamnan ya yabawa manyan ‘ya’yan jihar da suka bayar da gudunmawa ga ci gaban Najeriya, ciki har da tsoffin Shugabannin Ƙasa Umaru Musa Yar’Adua da Muhammadu Buhari, tare da wasu fitattun alkalai da malamai.
Ya ce gwamnatin jihar ta ƙarfafa tsarin tsaro ta hanyar ɗaukar aiki, horaswa da tanadar kayan aiki ga jami’an Katsina State Community Watch Corps domin su taimaka wa jami’an tsaro na hukuma wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Radda ya kuma yabawa sojoji, ‘yan sanda da jami’an Community Watch Corps kan nasarorin da suka samu a hare-haren baya-bayan nan, inda ya ce an kashe sama da ’yan bindiga 40, ciki har da wani fitaccen jagoransu. Ya gargadi ’yan siyasa da su guji amfani da mutuwar marasa laifi domin neman anfani na siyasa, yana mai jaddada cewa rayuwar ɗan Adam ta fi komai muhimmanci.