Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai‘Yan fashi sun harbe ɗalibar jami’ar jihar Nasarawa

‘Yan fashi sun harbe ɗalibar jami’ar jihar Nasarawa

Al’umma, ‘yan uwa da ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Lafia (FULAFIA) sun yi bankwana da ɗalibar aji na ƙarshe a sashen Chemistry, Habiba Ummi Lele, wadda ake zargin ’yan fashi da makami sun harbe har lahira a jihar Nasarawa.

Al’umma, ‘yan uwa da ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Lafia (FULAFIA) sun yi bankwana da ɗalibar aji na ƙarshe a sashen Chemistry, Habiba Ummi Lele, wadda ake zargin ’yan fashi da makami sun harbe har lahira a jihar Nasarawa.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da Habiba ke dawowa Lafia daga garin Keffi bayan halartar bikin yaye wata kawarta a Kwalejin Lafiya da Fasaha. Ana zargin ’yan fashin sun buɗe wa motar da take ciki wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta nan take.

An gudanar da sallar jana’izarta a ranar Lahadi tare da halartar jami’an gwamnati, ‘yan uwa, abokai da al’ummar yankin, inda aka yi mata addu’o’i tare da jajanta wa iyalanta kan wannan babban rashi.

Mutuwar Habiba ta haifar da jimami a kafafen sada zumunta, yayin da mutane da dama suka bayyana damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara ta’azzara, musamman a tsakanin ɗaliban jami’o’i a jihar Nasarawa.

Lamarin ya sake ƙara tada hankalin jama’a bayan sace wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Lafia kwanaki kaɗan da suka gabata, lamarin da ya sa ɗalibai da mazauna yankin ke kira ga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar da su ƙara matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments