Tsohon ɗan wasan tsakiya na kungiyar Barau FC, Nana Kwame Abraham, ya koma ƙungiyar AS GNN (Association Sportive de la Garde Nationale) ta gasar Super Ligue ta Jamhuriyar Nijar domin buga kakar wasa mai zuwa.
Ɗan wasan ɗan ƙasar Ghana mai shekara 23 ya yi fice a kakar 2025/2026 ta Gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL), inda ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Barau FC ta kammala kakar a matsayi na takwas tare da kai wa wasan kusa da na ƙarshe na Kofin Shugaban Ƙasa.
Abraham ya tabbatar da komawarsa sabon kulob ɗin ta shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara guda da zai ci gaba har zuwa ƙarshen kakar wasa mai zuwa.
Ya ce kafin wannan sauyi ya buga wa ƙungiyoyin Barau FC da Chanji FC na Kano wasa, sannan ya gode wa masoyansa bisa addu’o’i da goyon bayan da suka ba shi, yana mai cewa zai yi ƙoƙarin faranta musu rai.
A baya, Abraham ya taɓa bugawa AS Garde Nationale wasa, inda ya lashe Gasar Firimiya ta Nijar da Kofin Nijar. Haka kuma ƙungiyar ta wakilci ƙasar a gasannin nahiyar Afirka, ciki har da CAF Champions League da CAF Confederation Cup.