Tsohon Akbishop na Abuja kuma Kardinal, John Onaiyekan, ya bayyana damuwa cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da ƙudurin ci gaba da mulki bayan zaɓen 2027 “ta kowace hanya”, yana mai gargadin cewa ƙarfin iko da albarkatun gwamnati na iya shafar sahihancin zaɓe.
Onaiyekan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise TV, kwanaki kaɗan bayan shugabannin Ƙungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) sun gana da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce limaman cocin sun shaida wa shugaban ƙasar cewa Najeriya na fuskantar matsaloli masu tsanani, musamman ta fuskar tattalin arziki da ke ƙara jefa talakawa cikin wahala. A cewarsa, wasu mutanen da ke kewaye da shugaban suna gabatar masa da kyakkyawan hoto na halin da ƙasar ke ciki, wanda bai yi daidai da abin da al’umma ke fuskanta ba.
Onaiyekan ya ce Shugaba Tinubu bai amince da wannan tantancewa ba, inda ya nace cewa tattalin arzikin ƙasar na samun daidaito kuma Najeriya ba ta cikin halin da limaman suka bayyana. Ya ƙara da cewa hakan ya fito fili daga martanin da shugaban ya bayar yayin ganawar.
Kardinal ɗin ya kuma bayyana damuwa kan zaɓen 2027, yana mai cewa limaman Katolika na fargabar gwamnati na son amfani da damar da take da ita wajen tabbatar da ci gaba da mulki. Ya yi gargadin cewa idan ba a tabbatar da zaɓe mai gaskiya da adalci ba, inda ƙuri’un jama’a za su yi tasiri, hakan na iya haifar da ƙarin matsaloli ga ƙasar.