Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya sanar da janye kudirin sayar da wani ɓangare na hannun jarin Gasar Kofin Duniya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Infantino ya bayyana cewa kudirin ya haifar da ra’ayoyi mabambanta daga masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa.
Ya ce duk da cewa an kirkiro shirin ne da kyakkyawar niyya domin bunƙasa gasar da samar da ƙarin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, ya ga ya dace a janye shi domin a ci gaba da haɗin kai da kare muradun ƙwallon ƙafa ta duniya.
Infantino ya ƙara da cewa FIFA za ta ci gaba da tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo hanyoyin da za su ƙara bunƙasa gasar ba tare da haifar da sabani ba.