Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaNa yi nadamar zaben Atiku a matsayin mataimakin shugaban ƙasa – Obasanjo

Na yi nadamar zaben Atiku a matsayin mataimakin shugaban ƙasa – Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da yake nadama a rayuwarsa ta siyasa shi ne zaɓen Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Obasanjo ya yi wannan furuci ne a Legas yayin ƙaddamar da gidauniyar fitaccen ɗan nishaɗi Charly Boy da kuma littafin tarihin rayuwarsa.

A cewarsa, da ace ya san wasu halaye da ɗabi’un Atiku tun kafin zaɓensa, da bai taɓa zaɓarsa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa ba.

Sai dai ya ce yana gode wa Allah saboda, a cewarsa, abubuwan da suka faru tsakaninsu ba su hana gwamnatinsa cimma manufofin da ta sa a gaba ba, kuma ba su yi wa Najeriya illa ba.

Obasanjo ya kuma bayyana cewa duk da sabanin siyasar da ya shiga da Atiku, ba ya ɗauke da ƙiyayya ko gaba a zuciyarsa, yana mai cewa kowa ya yi abin da ya ga ya dace, yayin da shi kuma ya ci gaba da tafiyar da gwamnati bisa abin da ya yi imani da shi.

Obasanjo da Atiku sun yi aiki tare a matsayin shugaban ƙasa da mataimakinsa tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007, kafin daga bisani dangantakarsu ta lalace sakamakon rikice-rikicen siyasa da suka janyo zarge-zarge tsakanin ɓangarorin biyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments