Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya yi gargadi ga duk masu neman bizar shiga ƙasar da su guji amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) ko wasu manhajojin gyaran hoto wajen shirya hoton fasfo.
A cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar, ya bayyana cewa hotunan da aka yi wa kwaskwarima ta amfani da AI ko wasu hanyoyin gyaran hoto ba za su cika ƙa’idodin neman bizar Amurka ba.
Sanarwar ta ce dole ne hoton fasfo ya kasance sabon hoto da aka ɗauka cikin watanni shida da suka gabata, kuma ya nuna kamannin mai neman biza yadda yake a zahiri domin jami’an shige da fice su iya tantance shi cikin sauƙi.
Ofishin ya kuma yi gargaɗin cewa gabatar da hoton da aka yi wa gyara na iya janyo tsaiko wajen aiwatar da buƙatar neman biza ko kuma a buƙaci mai nema ya sake gabatar da sabon hoto da ya dace da ƙa’idoji.
Hukumar ta shawarci masu neman biza da su bi dukkan ƙa’idojin da aka gindaya domin kauce wa jinkiri ko matsaloli yayin gudanar da aikace-aikacen neman biza.