Dakarun Brigade ta 4 ta Rundunar Sojin Najeriya ƙarƙashin tawaga ta 83 sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Jihar Edo.
An sace mutanen ne a ranar 30 ga Yuli, 2026, a kan babbar hanyar Lagos–Benin da ke Ƙaramar Hukumar Ovia North East, inda wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka tare su.
A wata sanarwa da kakakin Brigade ta 4, Laftanar Kanal Kennedy Anyanwu, ya fitar, ya ce dakarun sun samu sahihan bayanan sirri game da lamarin yayin sintiri, lamarin da ya sa suka bi sawun masu garkuwa da mutanen.
Ya ce matsin lambar da sojojin suka yi ya tilasta wa masu garkuwa da mutanen tserewa cikin daji tare da barin mutum 11 daga cikin waɗanda suka sace.
A ranar 31 ga Yuli, sojojin sun ci gaba da bincike a cikin daji, inda suka samu nasarar ceto sauran mutum uku, wanda ya kawo adadin waɗanda aka ceto zuwa 14. Ya ƙara da cewa dukkansu suna cikin koshin lafiya kuma an haɗa su da iyalansu, yayin da ake ci gaba da farautar waɗanda suka tsere.
Anyanwu ya buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar Edo.