Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMatsalar haihuwa ce ta sa na saki Maimuna – Adam A. Zango

Matsalar haihuwa ce ta sa na saki Maimuna – Adam A. Zango

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya bayyana abin da ya haddasa rabuwarsa da matarsa, Maimuna Musa, bayan kwanaki ana ta yaɗa jita-jita da hasashe a kafafen sada zumunta.

A cikin wani gajeren bidiyo da ya wallafa, jarumin ya ce bambancin ƙwayoyin halitta da suka shafi haihuwa ne ya sa aurensu ya zo ƙarshe, ba rikici ko wata matsala ta daban ba.

Adam A. Zango ya ce ya ga ya dace ya fito ya yi wannan bayani domin dakatar da rade-radin da ake yi game da lamarin, yana mai roƙon jama’a da masoyansa su mutunta sirrinsu tare da guje wa yaɗa bayanan da ba su da tushe.

Jarumin ya kuma yi kira ga mabiyansa da su ci gaba da yi musu addu’a, yana fatan Allah Ya sauƙaƙa al’amura tare da ba kowa mafificin alheri

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments