Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKwankwaso ya karɓi lambar yabo ta kishin ƙasa da jagoranci a dimokuraɗiyya

Kwankwaso ya karɓi lambar yabo ta kishin ƙasa da jagoranci a dimokuraɗiyya

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya karɓi lambar yabo ta kishin ƙasa da jagoranci a dimokuraɗiyya daga ƙungiyar The Patriots Forum (PF).

Rahotanni sun ce an miƙa masa wannan karramawa ne a ranar Laraba, 29 ga Yulin 2026, domin girmama gudunmawar da ya bayar wajen inganta shugabanci nagari, hidimar jama’a da kuma bunƙasa dimokuraɗiyya a Najeriya.

Masu shirya bikin sun bayyana cewa an zaɓi tsohon gwamnan jihar Kano ne bisa irin rawar da ya taka a harkokin shugabanci da jajircewarsa wajen ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Sun kuma ce lambar yabon na daga cikin karramawar da ƙungiyar The Patriots Forum ke bayarwa tare da haɗin gwiwar National Orientation Agency (NOA) ga fitattun mutane da suka bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments