Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroYan bindiga sun harbe Kanal din soja har lahira a gidansa dake...

Yan bindiga sun harbe Kanal din soja har lahira a gidansa dake Abuja

Wani babban jami’in Rundunar Sojin Najeriya mai muƙamin Kanal, Abdussalam Ude, ya rasu bayan wasu ’yan bindiga sun kai masa hari a gidansa da ke unguwar Kurudu, Abuja.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, jim kaɗan bayan Kanal Ude ya dawo daga wurin aiki. Ana zargin maharan sun yi yunƙurin sace shi ko kuma wani daga cikin iyalansa, kafin daga bisani su harbe shi, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

A harin, matarsa, direbansa da jami’in tsaronsa sun samu raunukan harbin bindiga, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Marigayin, wanda ya fito daga Jihar Enugu, ya kasance jami’i a Nigerian Army Intelligence Corps, inda ya taka muhimmiyar rawa a fannin tattara bayanan sirri da yaƙi da ta’addanci. Haka kuma ya taɓa aiki a ayyukan soji a Arewa maso Gabashin Najeriya da kuma ƙasashen Chadi da Faransa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar Sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, yayin da jami’an tsaro suka fara bincike domin gano waɗanda suka kai harin da kuma musabbabin lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments