Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKashi 29 na malamai na shirin ajiye aiki saboda matsalar tsaro a...

Kashi 29 na malamai na shirin ajiye aiki saboda matsalar tsaro a Jihar Borno

Wani sabon rahoto da Cibiyar Nazarin Tattalin Arzikin Afirka (CSEA) ta fitar ya nuna cewa kusan kashi 29 na malaman makarantu a yankunan da rikici ya shafa a jihar Borno na fama da matsanancin damuwa, lamarin da ke sa da dama daga cikinsu tunanin barin aikin koyarwa.

Rahoton ya danganta matsalar da ci gaba da rashin tsaro, gudun hijira da kuma yawaitar katse harkokin ilimi a yankunan da rikicin ya fi shafa.

Binciken ya gudana a Maiduguri, Jere da Konduga, inda aka tattara bayanai daga gidaje, makarantu da sauran masu ruwa da tsaki.

Haka kuma, rahoton ya nuna cewa kusan rabin makarantu sun taɓa rufewa sakamakon rikici, yayin da kashi 65 na gidaje ke da aƙalla yaro ɗaya da ba ya zuwa makaranta.

An kuma bayyana cewa yawan ’yan mata masu barin karatu ya fi na maza.

Masu binciken sun yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar na iya ƙara raunana tsarin ilimi a yankin.

Sun ba da shawarar ɗaukar ƙarin malamai, ƙara horas da su kan kula da lafiyar kwakwalwa, faɗaɗa shirye-shiryen koyarwa a yankunan da rikici ya shafa, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin farar hula domin farfaɗo da ilimi a Arewa maso Gabas.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments