A kokarin ta na inganta bangaren sha’anin kiwon lafiya lafiya, Jami’ar Iconic ta gana da Hukumar Kula da Jami’an Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Najeriya (CHPRBN) a wani ɓangare na ƙudurinta na cika sharuɗɗan da ake buƙata don cigaba da gudanar da Digiri na Farko a Kimiyyar Kiwon Lafiyar Al’umma (B.CHS.) da kuma babbar Difiloma (Postgraduate Diploma in Community Health Education).
Wannan matakin yana nuna jajircewar Jami’ar na tabbatar da cewa dukkan kwasa-kwasanta sun cika ƙa’idodi da hukumomin da ke kula da sana’o’in kiwon lafiya da ma wasu bangarora suka gindaya.
Da yake jawabi a wajen taron, Babban Sakatare/Shugaban Zartarwa na CHPRBN, Dokta Bashir Idris, ya yaba wa Jami’ar Iconic bisa ƙudurinta na faɗaɗa damar samun ilimin kiwon lafiyar al’umma a Najeriya.
Ya yaba wa Jami’ar bisa hangen nesan ta na kafa kwasa-kwasan Digiri na Farko a Kimiyyar Kiwon Lafiyar Al’umma, yana mai cewa wannan tsari ya zo dai-dai da lokacin kuma ya dace da manufar Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin ƙasar.
Dokta Idris ya kuma lura cewa faɗaɗa damar horar da ma’aikatan kiwon lafiyar al’umma, musamman ta hanyar open and distance learning watau karatu daga nesa, zai taimaka wajen magance ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan lafiya, musamman a yankunan da ba a kula da su ba da kuma karkara.
Ya kuma tabbatar wa Jami’ar cewa Hukumar a shirye take ta ba da gudunmawa ga wadannan kwasa-kwasai.
Jami’ar Iconic jami’a ce mai zaman kanta wadda Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba ta cikakken lasisi da amincewa ta hannun Hukumar Jami’o’in Ƙasa (NUC). Jami’ar ta kuma sami amincewar NUC ga dukkan kwasa-kwasan ta da take gudanarwa.