Sunday, October 18, 2026
HomeIlimiJihar Edo ta rungumi fasahar zamani wajen inganta koyo da koyorwa

Jihar Edo ta rungumi fasahar zamani wajen inganta koyo da koyorwa

Gwamnatin Jihar Edo ta sake jaddada aniyarta ta faɗaɗa koyarwa ta hanyar fasahar zamani da inganta ilimin da ya dogara da fasaha, tana mai cewa ƙirƙire-ƙirƙire na da muhimmiyar rawa wajen shirya ɗalibai domin buƙatun tattalin arziƙin ƙarni na 21.

Gwamnatin Jihar Edo ta sake jaddada aniyarta ta faɗaɗa koyarwa ta hanyar fasahar zamani da inganta ilimin da ya dogara da fasaha, tana mai cewa ƙirƙire-ƙirƙire na da muhimmiyar rawa wajen shirya ɗalibai domin buƙatun tattalin arziƙin ƙarni na 21.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da shirin Electronic Education Initiative (E-DON) wanda TETFund ta ɗauki nauyinsa a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical) da ke Ekiadolor a Jihar Edo.

Mai ba Gwamna Monday Okpebholo shawara kan harkokin ɗalibai da wayar da kan jama’a, Victor Ureshemi Akande, ya ce samar da E-DON 98-inch QR Interactive Smart Board da manhajar koyarwa ta 3D Animation da ke cikinsa, babban mataki ne wajen inganta koyarwa da koyo ta amfani da fasahar cikin gida.

Ya ce ɗalibai sun cancanci samun kayan koyarwa na zamani masu inganci domin ba su ilimi, ƙwarewa da basirar da za ta taimaka musu wajen yin gogayya a duniya. Ya ƙara da cewa kirkirarriyar fasahar AI da fasahar zamani sun zama muhimman ginshiƙai a tsarin ilimi na yau.

Akande ya ce gwamnatin Gwamna Okpebholo, ta hanyar ajandar SHINE, za ta ci gaba da tallafa wa koyarwa ta zamani, ƙirƙire-ƙirƙire na cikin gida da bunƙasa ɗalibai a manyan makarantu.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da samar da haɗin gwiwa domin faɗaɗa damar samun kayayyakin koyarwa na zamani da kayan fasahar ilimi a manyan makarantu da makarantun firamare da sakandare.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments