Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnati ta ƙaddamar da shirin jawo ƙwararrun likitocin Najeriya daga ƙasashen waje

Gwamnati ta ƙaddamar da shirin jawo ƙwararrun likitocin Najeriya daga ƙasashen waje

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta yi amfani da shirin Diaspora Health Impact Initiative (DHII) 2026 wajen inganta harkar kiwon lafiya a Najeriya ta hanyar amfani da ƙwarewar likitocin Najeriya sama da 50,000 da ke ƙasashen waje, da kuma dubban ma’aikatan jinya, masu harhada magunguna da ƙwararrun lafiyar jama’a.

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta yi amfani da shirin Diaspora Health Impact Initiative (DHII) 2026 wajen inganta harkar kiwon lafiya a Najeriya ta hanyar amfani da ƙwarewar likitocin Najeriya sama da 50,000 da ke ƙasashen waje, da kuma dubban ma’aikatan jinya, masu harhada magunguna da ƙwararrun lafiyar jama’a.

Ministan Ƙasa na Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye, ya bayyana hakan ne a bikin Ranar ’Yan Najeriya da ke Ƙasashen Waje ta 2026 da aka gudanar a Abuja, mai taken: “Amfani da Ƙwarewar ’Yan Najeriya da ke Ƙasashen Waje wajen Ƙarfafa Tsarin Kiwon Lafiya na Cikin Gida domin Bunƙasa Ƙasa.”

Ya ce shirin DHII zai taimaka wajen musayar ilimi, gudanar da ayyukan jinya na musamman, horar da ma’aikatan lafiya, jagoranci a fannin aikin likita, bincike da bunƙasa ma’aikatan kiwon lafiya.

A nata ɓangaren, Shugabar Hukumar ’Yan Najeriya da ke Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce hukumar ta samu ci gaba daga tsara manufofi zuwa aiwatar da ayyukan da ke kawo tasiri tun daga shekarar 2019.

Ta ce ƙungiyoyin likitocin da ke ƙasashen waje sun gudanar da ayyukan jinya a dukkan shiyyoyin siyasa shida na ƙasar, tare da taimaka wa asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya ta hanyar samar da kayan aiki da gudunmawar da ta kai daruruwan miliyoyin naira.

Dabiri-Erewa ta kuma ce kuɗaɗen da ’yan Najeriya ke aikowa daga ƙasashen waje sun ƙaru daga dala biliyan 17 a shekarar 2019 zuwa sama da dala biliyan 21 a 2025, yayin da gwamnati ke shirin ƙaddamar da wasu shirye-shiryen zuba jari da gidaje masu sauƙin samu ga ’yan Najeriya da ke ƙasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments