Akanta Janar na Tarayyar Najeriya, Dakta Shamseldeen Ogunjimi, ya bayyana cewa an yi amfani da wata takardar bogi da aka danganta da Fadar Shugaban Ƙasa wajen neman amincewar gwamnati domin kafa wata hukuma mai suna Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC).
Ya bayyana hakan ne yayin da yake ba da shaida a gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken yadda aka kafa hukumar da kuma ayyukan da ta gudanar.
A cewarsa, ofishinsa ya karɓi wasiƙar ne a watan Nuwamban 2024, mai ɗauke da lambar Fadar Shugaban Ƙasa, inda aka nemi a ƙirƙiri lambar gudanarwa (Administrative Code) domin gudanar da harkokin kuɗi da kasafi.
Ogunjimi ya ce bisa tsarin aiki, ofishinsa ya amince da buƙatar tare da ƙirƙiro lambar gudanarwar, sai dai daga baya bincike ya tabbatar da cewa wasiƙar ba daga Fadar Shugaban Ƙasa ta fito ba, illa dai takarda ce ta bogi.
Ya ƙara da cewa daga bisani hukumar ta nemi a ba ta damar buɗe asusun gwamnati, ta riƙa sarrafa kuɗinta da kanta, tare da neman a tura mata ma’aikata.
Sai dai ya jaddada cewa ba a taɓa fitar da ko kwabo ɗaya daga baitul malin gwamnati zuwa asusun hukumar ba.
Haka kuma, ya bayyana cewa hukumar ta nemi tallafin kafa ofis na Naira biliyan 27.4, amma gwamnatin tarayya ta yi watsi da buƙatar saboda babu tanadin kuɗin a cikin kasafin kuɗi.
A cewarsa, ko da yake Babban Bankin Najeriya (CBN) ya buɗe wa hukumar wasu asusun kuɗaɗen ƙasashen waje guda biyu, ba su fara aiki ba saboda hukumar ta kasa cika sharuɗɗan da ake buƙata.
Kwamitin Majalisar Wakilai ya ce ya gano sama da takardu 29 da ake zargin an ƙirƙira domin yaudarar hukumomin gwamnati.
Haka kuma, rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ake zargi da jagorantar hukumar, Adeyemi Adeniyi, a gaban kotu bisa zargin damfara da amfani da takardun bogi.
Majalisar Wakilai ta kuma umarci Sufeto Janar na ’Yan Sanda da ya gabatar da Adeyemi Adeniyi a gabanta nan da ranar Laraba domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa.