Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAn kama matashiya da ake zargi da yanke mazakutar saurayinta a Kano

An kama matashiya da ake zargi da yanke mazakutar saurayinta a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama wata matashiya mai shekaru 25 da ake zargi da yanke mazakutar saurayinta yayin da yake barci a wani otal da ke unguwar Badawa a birnin Kano.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Litinin.

Ya bayyana cewa duk da cewa masoyan biyu ’yan asalin Jihar Jigawa ne, abin ya faru ne a Kano.

A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa wadda ake zargin ta zo daga Maigatari ɗauke da wata wuƙa, wadda ake zargin ta yi amfani da ita wajen aikata laifin.

Ta kuma shaida wa jami’an ’yan sanda cewa ta aikata hakan ne bayan saurayin ya sha maganin ciwon kai kuma ya yi barci mai nauyi.

Rahotanni sun ce bayan aukuwar lamarin, ana zargin matar ta ja saurayin zuwa banɗaki domin wanke jinin kafin mutanen da ke kusa suka lura da abin da ke faruwa tare da sanar da jami’an tsaro.

Rundunar ta ce har yanzu babu wata hujja da ke tabbatar da rahotannin da ke yawo cewa an yi amfani da wani sinadari ko kayan maye.

Sai dai jami’an bincike sun kwato kwalbar abin sha da ruwa daga ɗakin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin tantance ko suna da alaƙa da abin da ya faru.

’Yan sanda sun tabbatar da cewa saurayin yana raye kuma yana ci gaba da karɓar magani a asibiti, yayin da ake tsare da wadda ake zargin domin ci gaba da bincike kafin gurfanar da ita a gaban kotu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments