Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sanar da shirin gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa wasu dillalan gidaje da masu gidajen haya na ƙara wa jama’a kuɗaɗen da suka wuce kima.
An bayyana cewa matakin ya biyo bayan yawaitar ƙorafe-ƙorafen da mazauna jihar suka gabatar, inda suka ce irin waɗannan ƙarin kuɗaɗe na sa samun gidaje da filaye ya ƙara zama mai wahala.
Sakataren yaɗa labaran Majalisar, Kamalu Sani Shawai, ya ce za a yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin gudanar da bincike mai zurfi.
Ya ƙara da cewa Majalisar za ta kuma nazarci yiwuwar sake duba dokar da ke tafiyar da harkokin dillalan gidaje domin samar da mafita ga matsalar da kuma kare muradun jama’a.