Rahotanni sun ce maharan sun kai farmakin ne da safiyar ranar Laraba yayin da manoman ke gudanar da ayyukansu a gonaki. Shaidu sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun iso ne kan babura da dama kafin su rika harbin duk wanda suka tarar a wurin.
Akalla manoma 23 ne suka rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a gonakinsu da ke gundumar Sauna, a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.
Tun da farko, rundunar ‘yan sandan Zamfara ta tabbatar da harin, inda kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce mutane 15 ne aka tabbatar sun mutu a lokacin da aka samu rahoton farko.
Sai dai majiyoyi daga yankin sun ce an sake gano karin gawarwaki a gonaki, lamarin da ya sa adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 23.
Wani mazaunin yankin ya ce an yi jana’izar dukkan wadanda aka kashe a ranar Alhamis, inda aka binne su tare a makabartar kauyen Sauna.
DSP Yazid Abubakar ya ce jami’an tsaro sun bazama yankin domin dawo da zaman lafiya tare da daukar matakan hana sake afkuwar irin wannan hari.