Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da umarnin gudanar da bincike kan yadda ake amfani da kuɗaɗen tallafin tsaro na wata-wata da ake bai wa ƙananan hukumomi.
Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne bayan wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisar mai wakiltar mazabar Ghari/Tsanyawa, Garba Gwarmai, ya gabatar a zaman majalisar da Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Isma’il Falgore, ya jagoranta.
Da yake gabatar da ƙudirin, Gwarmai ya ce hare-haren da ake zargin ‘yan bindiga ne ke kai wa al’ummomin da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa sun ƙara tsananta. Ya ce matsalar tsaron ta shafi noma, ilimi, harkokin lafiya da kasuwanci a yankin.
Ya shaida wa majalisar cewa sabon harin ya faru ne a ƙauyen Yan Cibi da ke gundumar Yan Kamaye, inda ake zargin ‘yan bindiga sun yi ƙoƙarin sace mutane tare da kwashe dabbobi, kafin jami’an tsaro su dakile harin.
A cewarsa, harin ya yi sanadin rasuwar shugaban al’umma kuma ɗan ƙungiyar sa-kai, Yusuf Adamu, yayin da wasu mazauna yankin suka samu raunukan harbin bindiga, kuma suna ci gaba da karɓar magani a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad.
Gwarmai ya yaba wa sojoji da ‘yan sanda saboda nasarar da suka samu wajen ƙwato dabbobi da dama da aka sace. Sai dai ya ce jami’an tsaron sun kasa bin maharan saboda wahalar yanayin hanyar da ke kan iyakar Kano da Katsina.
Ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da gwamnatin tarayya su ƙara ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa ta hanyar tura ƙarin jami’an tsaro tare da samar musu da kayan aiki da tallafin da suke buƙata.
Har ila yau, Gwarmai ya nuna shakku kan yadda ake amfani da kuɗaɗen tallafin tsaro na wata-wata da ake bai wa ƙananan hukumomi. Ya yi zargin cewa jami’an tsaro a yankin ba su da isassun kayan aiki duk da cewa ana fitar da kuɗaɗen.
Ya tunatar da majalisar cewa tun da farko ta umarci ƙananan hukumomin da abin ya shafa su gabatar da rahotannin yadda suka kashe kuɗaɗen tsaron, amma har yanzu ba su cika wannan umarni ba.
Bayan tattaunawa, majalisar ta umarci kwamitin da abin ya shafa da ya binciki yadda aka yi amfani da kuɗaɗen tsaron tare da tabbatar da an yi musu amfani cikin gaskiya da riƙon amana.
Majalisar ta kuma buƙaci gwamnatin jihar Kano da gwamnatin tarayya su ɗauki matakan gaggawa domin ƙarfafa tsaro a al’ummomin da ke kan iyaka, musamman a ƙananan hukumomin Tsanyawa da Bagwai, domin hana sake aukuwar hare-hare da kuma dakile yaɗuwar matsalar tsaro zuwa sauran sassan jihar.