Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kafa kamfanin jirgin sama mallakin jihar mai suna “Kano First” domin inganta harkokin sufuri da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron Majalisar Zartarwar Jihar Kano da aka gudanar ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Kano.
A cewarsa:
“Mun yi alkawari, da yardar Allah, za mu kafa kamfanin jirgin sama wanda za mu saka masa suna ‘Kano First’ domin ci gaban jiharmu.”
Ya ce shirin na daga cikin manufofin gwamnatin jihar na inganta harkokin sufurin jiragen sama, jawo hannun jari, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa matsayin Kano a matsayin cibiyar kasuwanci da sufuri a Arewacin Najeriya.