Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna Credit for Laptops, Internet, Connectivity and Knowledge Digital Devices (C.L.I.C.K.D.), domin bai wa ‘yan Najeriya damar samun kwamfutocin tafi-da-gidanka (laptops) da sauran na’urorin zamani ta hanyar rancen kuɗi mai sauƙin biya.
Shirin na gudana ne ta hannun Hukumar Ba da Rance ta Ƙasa (CREDICORP) tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Sadarwa, Ƙirkire-ƙirkire da Tattalin Arzikin Zamani ta Tarayya.
A matakin farko, shirin zai bai wa mahalarta 3 Million Technical Talent (3MTT) damar samun kwamfutocin da aka haɗa a Najeriya, kafin daga bisani a faɗaɗa shirin zuwa sauran na’urorin zamani.
Da yake ƙaddamar da shirin a Abuja, Ministan Sadarwa, Ƙirkire-ƙirkire da Tattalin Arzikin Zamani, Dr. Bosun Tijani, ya ce shirin zai sauƙaƙa wa matasa da sauran masu sha’awar fasaha samun kayan aikin da suke buƙata, tare da ƙarfafa tattalin arziki, bunƙasa kasuwanci da samar da ayyukan yi.
A cewarsa, an fara rabon kwamfutocin ne a Abuja inda mutum 77 suka karɓi na’urorinsu, yayin da za a ci gaba da aiwatar da shirin a sauran jihohin ƙasar a matakai daban-daban.