Ƙungiyar North Central Agenda (NCA) mai fafutuka kan harkokin siyasa ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a karo na biyu a zaɓen 2027.
Da take jawabi a taron yini guda da aka gudanar a Abuja kan ci gaban yankin Arewa ta Tsakiya ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda, shugabar taron, Ene Ogbole, ta ce nasarar Tinubu a yankin a zaɓen 2027 abu ne tabbatacce.
Ta kuma yi watsi da sabon suka kan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa Musulm-Musulm ta jam’iyyar APC, tana mai cewa ‘yan Najeriya sun riga sun yanke hukunci kan batun tun a zaɓen 2023.
Ogbole ta ce yankin Arewa ta Tsakiya ya shafe shekaru yana fama da ƙarancin ababen more rayuwa da matsalar tsaro kafin Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023.
A cewarta, gwamnatin ta zuba jari a hanyoyi, noma, ilimi da tsaro. Ta lissafo manyan ayyuka da suka haɗa da titin Calabar zuwa Abuja ta Ebonyi, Benue, Kogi da Nasarawa, titin Sokoto zuwa Badagry, titin Akwanga zuwa Maiduguri ta Jos, Bauchi da Gombe, hanyar Suleja zuwa Minna da kuma aikin faɗaɗa hanyar Lokoja zuwa Okene.
Ta kuma yaba da tallafin da ake bai wa ilimi ta hannun TETFund da NELFUND, tana cewa hakan ya faɗaɗa damar samun ilimi tare da kawo ƙarshen yawan yajin aikin da ake yi a manyan makarantu. A cewarta, ingantaccen tsaro ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu, yayin da kasuwanci ke ci gaba da farfaɗowa.
Ta ƙara da cewa ƙungiyar za ta wayar da kan al’umma tare da tattara goyon baya a jihohin Arewa ta Tsakiya shida da Babban Birnin Tarayya domin tabbatar da sake zaɓen Tinubu.