Ofishin Ministan Tsaron
Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa yana shirin yin murabus daga mukaminsa.
A cikin wata sanarwa da Mataimakiyarsa ta Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Leah Katung-Babatunde, ta fitar a ranar Litinin, ofishin ya bayyana cewa rahotannin ba su da tushe balle makama, tare da bayyana su a matsayin ƙarya tsagwaronta.
Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su yi watsi da irin waɗannan jita-jita, tana mai jaddada cewa Janar Christopher Musa na ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda aka saba.