Kwamishinan ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT), CP Ahmed Sanusi, ya gargadi mazauna Abuja, musamman matasa, da kada su amince jami’an ’yan sanda su binciki wayoyinsu yayin sintiri ko binciken ababen hawa.
Ya bayyana cewa irin wannan bincike ba ya cikin umarnin da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayar, kuma ya jaddada cewa an haramta wa jami’an ‘yan sanda binciken wayoyin jama’a ba tare da sahihin dalili ko bin ka’idojin doka ba.
CP Ahmed Sanusi ya kuma bukaci jami’an ‘yan sanda su mutunta haƙƙin jama’a tare da gudanar da aikinsu bisa ƙa’idojin doka da ƙwarewar aikin ’yan sanda.