Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da ci gaba da samun nasarori a yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a sassan jihar.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa, ya fitar, ya ce hare-haren haɗin gwiwa da rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro suka gudanar a ƙananan hukumomin Anka, Gummi, Bukkuyum, Zurmi da wasu yankuna sun haifar da gagarumar nasara.
Sanarwar ta ce hare-haren sun taimaka wajen dawo da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da rage damar da masu aikata laifuka ke da ita wajen gudanar da ayyukansu.
Gwamna Dauda Lawal, ya yabawa jami’an tsaro bisa jarumtarsu, jajircewa da ƙwarewar da suke nunawa wajen tabbatar da tsaron jihar.
Ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da samar da dukkan tallafin kayan aiki da dabarun da ake buƙata domin ƙarfafa ayyukan tsaro da tabbatar da zaman lafiya a Zamfara.