Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (ICPC) ta musanta rahotannin da ke cewa ta kama Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, kan zargin badakalar da ta shafi hukumar PFIPC.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata, ICPC ta bayyana cewa Gbajabiamila bai shiga hannu ba, illa ya je hedkwatarta ne domin amsa gayyatar da aka yi masa a matsayin wani ɓangare na binciken da ake gudanarwa.
Hukumar ta buƙaci jama’a da kafafen yaɗa labarai su guji yaɗa rahotannin da ba su da tushe, tana mai jaddada cewa binciken na ci gaba da gudana bisa ƙa’idojin doka.