Akalla yara shida daga iyali guda sun mutu, yayin da wasu huɗu suka jikkata bayan tsawa ta same su a ƙauyen Dadiri-Tirgali, da ke gundumar Garum a ƙaramar hukumar Ganye ta jihar Adamawa.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Lahadi, a lokacin da aka samu ruwan sama mai ƙarfi. Yaran suna aikin girbin gyada a gona ne kafin su fake a ƙarƙashin wata bishiya domin guje wa ruwan sama.
Ba da jimawa ba, tsawa ta bugi bishiyar, inda ta kashe yara shida nan take tare da jikkata wasu huɗu. An kai waɗanda suka jikkata Babban Asibitin Ganye domin ba su kulawar lafiya.
Yaran da suka mutu sun haɗa da Abdulrahman Musa mai shekara 7; Aliyu Sule Maunde da Jaafar Sule Maunde, dukkaninsu masu shekara 10; Bilkisu Jibrin Maunde mai shekara 20; Musa Ahmadu mai shekara 9; da Auwalu Nuhu mai shekara 11.
Waɗanda suka jikkata su ne Nasiru Abubakar mai shekara 7; Rilwanu Ahmadu mai shekara 9; Sa’adatu Isa mai shekara 35; da Hasiya Isa mai shekara ɗaya da wata uku. Daga baya, an binne yaran shida a unguwar Wukari Ganye bisa tsarin addinin Musulunci.
Ɗaya daga cikin iyayen yaran, Musa Maude, ya ce shi ne ya tura su gona domin girbin gyada, amma daga baya ya samu kiran waya cewa tsawa ta same su. Da suka isa wurin, sai suka tarar da yaran kwance a ƙarƙashin bishiyar, wasu daga cikinsu ba sa motsi.
Wani mahaifi, Suleiman Maude, ya ce ‘ya’yansa biyu, Aliyu da Jaafar, na cikin waɗanda suka mutu. Ya bayyana cewa ya koma gida saboda ruwan sama, kafin a sanar da shi cewa tsawa ta afkawa yaran da ke gona.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Sa’adatu Isa, ta ce ta raka yaran zuwa gona tare da ‘yarta mai shekara ɗaya da wata uku. Bayan ruwan sama ya tsananta, ta umurci yaran da su fake a ƙarƙashin bishiya tare da amfani da laima guda ɗaya.
Ta ce ba da jimawa ba suka ji wata ƙara mai ƙarfi tare da wani haske mai tsananin haske, sannan ta faɗi sumammiya. Ta ce daga baya ta farfado, amma sai aka sanar da ita cewa yara shida sun rasa rayukansu.
Shugaban ƙaramar hukumar Ganye, Daniel Kamsobbi, ya tabbatar da mutuwar yara shida da jikkatar wasu huɗu. Ya ce an sallami uwa da ɗanta daga asibiti, yayin da wasu mutane biyu ke ci gaba da samun magani.
Kamsobbi ya ce majalisar ƙaramar hukumar ta umarci ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin lamarin da kuma gano matakan da za a ɗauka domin wayar da kan jama’a.
Masana muhalli sun shawarci manoma da jama’a da su guji fakewa ƙarƙashin bishiyoyi a lokacin tsawa. Sun ce ya fi kyau a nemi mafaka a cikin ƙaƙƙarfan gini, a nisanci fili, ruwa, tagogi, ƙofofi da kuma abubuwan ƙarfe har sai guguwar ta wuce.