Yara biyu ’yan’uwa sun rasa rayukansu bayan ambaliyar ruwa ta tafi da su a yayin da suke dawowa daga makarantar Islamiyya a garin Janbago, ƙaramar hukumar Katsina ta jihar Katsina.
Rahotanni sun ce Muhammad Salisu, mai shekaru 12, da ƙaninsa Abdurrahman Salisu, mai shekaru 7, sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke ƙoƙarin tsallaka wata hanyar ruwa da ambaliyar ruwa ta mamaye.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa a yankin, lamarin da ya sanya yaran suka kasa tsallakawa lafiya.
Mazauna yankin sun shiga cikin jimami bayan samun labarin mutuwar yaran biyu, waɗanda suka kasance ’yan gida ɗaya.
Lamarin ya sake jawo hankali kan haɗarin ambaliyar ruwa da ke barazana ga al’ummomi a lokacin damina, musamman yara da ke tafiya a kan hanyoyin da ruwa ya mamaye.