Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaINEC za ta fara karɓar sunayen ’yan takarar gwamna da mataimakansu yau...

INEC za ta fara karɓar sunayen ’yan takarar gwamna da mataimakansu yau Asabar

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) za ta fara karɓar sunayen ‘yan takarar gwamna da mataimakansu daga yau Asabar, a wani muhimmin mataki na shirye-shiryen tunkarar zaɓukan gwamnoni a jihohin da wa’adin shugabanninsu ke ƙarewa.

Fara karɓar sunayen na bai wa jam’iyyun siyasa damar kammala gabatar da sunayen ’yan takararsu da mataimakan da za su fafata a zaɓen, kamar yadda jadawalin hukumar ya tanada.

Ana sa ran wannan mataki zai ƙara zafafa harkokin siyasa, yayin da ake ci gaba da tattaunawa da shawarwari a tsakanin jam’iyyu kan zaɓen waɗanda za su tsaya takara da kuma mataimakansu.

A wasu jihohi, ana ta hasashen cewa wasu gwamnoni na iya sauya mataimakansu kafin zaɓe, yayin da wasu kuma ake sa ran za su ci gaba da tikitin da suka yi amfani da shi a wa’adin farko.

Sai dai babu wani tabbaci kan hakan har sai jam’iyyu sun miƙa sunayen ’yan takararsu ga INEC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments